BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Shettima ya kai ziyara Kwara bayan mummunan harin jihar
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Sabbin shafukan da ke nuna abin da mutane ke aikatawa a ɗakunan otal
Saurayi da budurwa da suka kwana a Shenzhen sun gano cewa an ɗauki bidiyonsu na kwanciyar aure a asirce kuma aka yaɗa ta zaurukan kafafen sada zumunta.
Bidiyo, Attajirin da ya fara kasuwanci da jarin naira 20, Tsawon lokaci 8,58
Cikin wata hira da BBC Alhaji Halliru ya ce ya fara kasuwancinsa ne a lokacin mulkin soji na tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo.
Matsalar tsaro ƙaruwa take yi ko raguwa a arewacin Najeriya?
"A shekarar 2025, mutum 10,504 aka kashe a Najeriya, sannan idan aka tattara alƙaluman mace-macen da aka samu a sassan Najeriya, kusan kashi 88 cikin ɗari na wannan adadin a arewacin Najeriya aka yi."
Abin da ya sa muka amince da ɓangaren Wike na PDP - INEC
Sabuwar taƙaddamar shugabancin PDP ta taso ne bayan ɓangaren Wike ya samu amincewar hukumar INEC saboda umarnin yin hakan da ya samo daga kotu, wanda kuma ɓangaren Tanimu Turaki ke cewa ba za ta saɓu ba.
Me ya sa ake taka-tsantsan a tattaunawar Iran da Amurka?
Wannan dai ita ce tattaunawa ta farko kai tsaye tun bayan yaƙin da ake kira "yaƙin kwanaki 12", wanda ya ɓarke bayan harin da Isra'ila ta kai wa Iran wanda ya haifar da fargabar ɓarkewar yaƙi yankin.
'Jihohin da aka fi kashe mutane a Najeriya cikin watan Janairu'
Kamfanin Beacon Security mai nazarin tsaro a yankin Sahel ya ce kimanin mutum 661 ne suka mutu, yayin da aka sace mutum 475 a watan farkon na sabuwar shekarar 2026.
Za mu yi ƙarar INEC saboda amincewa da ɓangaren Wike - PDP
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 6 ga watan Fabrairun 2026.
Mece ce aƙidar ƙungiyar mayaƙan Mahmuda, wadda ake zargi da hannu a harin Kwara?
Masana tsaro sun bayyana cewa akwai ƙungiyoyin ƴan bindiga da dama da ke gudanar da ayyukansu a dazukan arewa maso yammacin Najeriya, inda abin ya fi ƙamari a jihohin Neja da Kebbi da Zamfara da Sokoto da kuma Kaduna, sai dai abin ya fara ta'azzara a jihohin Kwara ko Kogi a baya-bayan nan.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 7 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 7 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 7 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Ra’ayi Riga, 19:29, 6 Fabrairu 2026, Tsawon lokaci 1,00,00
Shiri ne a duk ranar Juma'a da ke baiwa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu.
Wasanni
Hukumar ƙwallon Saudiyya ta gargaɗi Ronaldo
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 01 zuwa 06 ga Fabrairu 2026
Arsenal da Ac Milan na rige-rigen ɗaukar Goretzka, Saudiyya za ta raba gari ga Ronaldo
A shirye Saudyya take ta raba gari da Ronaldo, Chelsea za ta kara da Tottenham kan sayen Dusan Vlahovic, Arsenal za ta fafata da AC Milan don neman Leon Goretzka
Juventos ta ƙwallafa rai kan Tonali, wataƙila Lewandowski ya bar Barca
Dan wasan tsakiya na Newcastle United Sandro Tonali yana cikin jerin 'yan wasan da Juventus ke nema, Napoli za tsawaita kwantaragin Scott McTominay. Alejo Veliz, wanda ke zaman aro a Rosario Central, zai koma kulob din Bahia na Brazil.
Da alama Ronaldo ya shiga damuwa a Saudiyya
An fara tababa kan makomar Cristiano Ronaldo a ƙungiyarsa ta Al-Nassr bayan rashin ganinsa a wasan da ƙungiyar ta buga ranar Litinin da ƙungiyar Al-Riyadh a babbar gasar ƙasar ta Saudi Pro League.
Champions League: Benfica za ta ƙara fafatawa da Real Madrid a wasan cike gurbi
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Talata 27 zuwa 30 ga Janairun 2026
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Waɗanne ne mutanen da Saudiyya ta yarje wa shan barasa a ƙasar?
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun fara ɗage haramcin sayar wa masu kuɗi ƴan ƙasashen waje basara a ƙasar, a wani mataki na sauya dokar haramcin da aka sanya shekara 73 da suka gabata.
Ƙasashen Afirka biyu tal da suka mallaki jirgin yaƙin zamani na F-16
Bayanai sun nuna cewa ƙasashe biyu ne kacal a Afirka suke da jiragen yaƙi na zamani na F-16, wanda jirgi ne da ke cikin waɗanda suka fi ƙarfi da inganci a wajen yaƙi.
Gwamnonin arewa sun yi Alla-wadai da kashe-kashen Kwara, Katsina da Benue
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 5 ga watan Fabrairun 2026.
Abin da ke kunshe cikin bayanan binciken mutuwar Jeffrey Epstein
Epstein ya mutu a wani gidan yari na birnin New York ranar 10 ga watan Agustan 2019 yayin jiran shari'a.
Yadda gyaran dokar zaɓen Najeriya ke ci gaba da janyo takaddama
A ranar Laraba 4 ga watan Faburairu majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin dokar zaɓe ta 2022, bayan gyaran da ta yi mata, lamarin da ya janyo martani daga sassan Najeriya.
'Komai nawa ya ƙare saboda tsare ni shekara 11 babu sharia'
Lauyan Ja'o Sabo ya shaida wa BBC cewa tun a 2014 ne ƴan sanda suka kama magidancin bisa zargin fashi da makami da haɗa baki don aikata laifi amma ba a iya gurfanar da shi yadda ya kamata a kotu don yi masa shari'a ba.
Wane ne Jeffrey Epstein: hamshaƙin ‘kawalin’ shugabanni da attajiran duniya?
Sai dai har yanzu akwai masu zargin cewa akwai sauran bayanai da dama game da kundin da ba a bayyana ba.
Waɗanne dokokin zaɓe ne majalisar Najeriya ta amince a yi wa gyara?
Ɗaya daga cikin gyare-gyaren da aka yi wa dokar ta 2022 shi ne rage wa'adin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ke da shi na fitar da sanarwar jadawalin zaɓe daga kwana 360 zuwa 180.
'Mahara sun turo wasiƙa kafin kai hari a Kwara'
Gwamnatin Najeriya ta ɗauki wannan mataki ne bayan harin da aka kai wa ƙauyen Woro, inda rahotanni ke cewa an tattara gawarwakin mutane 78 da mahara suka kashe.
Ɓangarori biyar da gwamnati ta gaza kare fararen hula a Najeriya - Rahoto
Ƙungiyar ta Human Rights Watch ta ce matsalar tsaro ta ƙaru a faɗin Najeriya, wanda ta ce ya ƙara nuna rashin ƙoƙarin hukumomin ƙasar wajen kare rayukan al'umma.
Masoyan da aka yi wa 'kisan gilla' saboda bambancin addini
Ƴansanda sun ce an kashe su ne ta hanyar duka da cebur, kuma ana zargin cewa ƴan'uwan Kajal, maza, su uku ne ke da hannu, kuma tuni an kama su.
Tura sojojin Amurka Najeriya: Me hakan ke nufi ga tsaron ƙasar?
Jami'an Amurka da na Najeriya duk sun tabbatar da batun sai dai babu cikakken bayani kan adadin sojojin, yaushe suka isa Najeriya da kuma haƙiƙanin aikin da za su yi a ƙasar.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.































































